News
Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro 19 a Kebbi yayin ziyarar mataimakin gwamna

Daga mujahid danllami garba
Rahotanni daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro a kalla 19 a wani hari da suka kai a ƙauyen Kanya da ke cikin karamar hukumar Danko-Wassagu.
Maharan sun je ne a kan babura a lokacin da mataimakin gwamnan Kebbi ke ziyara a ƙauyen a ranar Talata.
Mataimakin gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya ce dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai faɗi yawan jami’an da aka kashe ba.
Mutanen da suka mutun sun haɗa da sojoji 13 da ƴan sanda biyar da wani ɗan sa kai.
Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi.
Harin ya faru ne kwana ɗaya bayan da ƴan bindiga suka kashe ƴan sa kai 63 a yankin.Yan bindiga sun kashe sojoji a Kebbi.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana hakan ne a lokacin da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ya ziyarci Birnin Kebbi, babban birnin Jihar a ranar Laraba.
Kisan sojojin ya faru ne kwana guda bayan da aka yi wa kimanin ‘yan banga 63 da aka fi sani da Yan-Sa-Kai kisan kiyashi a Zuru.
Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Umar Babale Yauri, wanda ya yiwa ministan bayani, bai bada adadin sojojin da aka kashe ba.
Ya kara da cewa gwamnati na kokarin ganin ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kudancin jihar.