News
Dabar siyasa a Kano: DSS ta gayyaci wasu manyan na hannun-daman Ganduje.

Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci wasu manyan na hannun-daman gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa mutanen sun kai kansu gaban DSS bisa zarginsu da hannu a dabar siyasa.
Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar ta Kano, Murtala Sule Garo, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya ce ba ya cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka mika kansu ga DSS.
A tattaunwarsa da BBC, Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano, ya ce yana cikin wadanda aka gayyata.
A cewarsa, an kuma gayyaci Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale; da shugaban karamar hukumar Kura, Mustafa Abdullahi; da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo; da masu bai wa gwamna shawara, Dakta Sabitu Shanono da Hajiya Maryam Kofar Mata.
Fa’izu Alfindiki ya kara da cewa DSS ta kuma gayyaci mutumin da ke son jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar ta Kano a zaben 2023, A.A Zaura, yana mai cewa “gayyatar da aka yi mana tana da alaka da yadda za a samu zaman lafiya a jihar Kano”
Amma rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikinsu da hannu a manyan-manyan hare-haren dabba, lamuran da suka yi sanadin mutuwar wasu mutane.
Jaridar Premium Times da ake wallafa wa a intanet ta ruwaito cewa wata arangama da aka yi tsakanin bangarorin wasu masu neman takarar gwamnan jihar a Kano ta yi sanadin mutuwar mutum hudu.
A baya bayan nan dai ‘yan siyasa musamman na jam’iyyar APC sun rika sukar juna bayan raba gari tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, sai dai tun kafin hakan an rika jifan juna da muggan kalamai da kuma amfani da ‘yan daba domin biyan bukatu na siyasa.
Hakan kuwa ya yi kamari ne bayan da mai dakin gwamnan jihar Kano, Hafsatu Ganduje, ta yi nuni da cewa Kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo ne ya dace ya gaji mjinta a zaben gwamna na 2023.
‘Yan siyasa da dama sun fassara kalaman da cewa alama ce ta cewa tuni aka ware ‘yan bora da ‘yan mowa kuma an rufe kofa ga duk wanda yake neman zama gwamnan jihar ta Kano a karkashin jam’iyyar APC. To amma daga bisani gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba a fahimci kalaman mai dakin gwamnan ba ne.
Tun daga wancan lokaci ne yanayin siyasa ya kara yin zafi tsakanin bangaren Murtala Sule Garo da kuma Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ake rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.
Kazalika hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke inda ta bai wa bangaren Ganduje nasara a shugabancin jam’iyyar APC a Kano ya ta’azzara yanayin siyasar da ake ciki a jihar.
Masana harkokin siyasa irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge sun ce kokawar neman iko na cikin abubuwan da suka ta’azzara amfani da ‘yan daba wajen cimma buri na siyasa.