News
NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki da Wahalar Man Fetur Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci
Daga yasir sani abdullahi
A yayin da kusan kowane bangare na rayuka ke kara dogaro da amfani da wutar lantarki, samuwar wutar sai kara wuya take a Najeriya, inda a halin yanzu bukatar wutar ke karuwa saboda matsanancin zafi da tsadar man fetur da Dizel.
Shirin Ya Labari Duniya na yau za muji yadda ku ke rayuwa a cikin duhu, rashin tabbacin samun wutar da kuma musabbabin matsalatar, wadda ta sa cibiyoyin kiwon lafiya, masana’antu, da sauran bangarori kokawa.
Kana kuma da yadda wahalar man fetur ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, ta ke shafar al’amuran kasuwanci da shiga cikin wani mawuyacin hali.