News
Rikicin APC: Buni ya mayar wa da El-Rufai martani

Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Rikicin jam’iyyar APC ya kara kamari biyo bayan wasikar da Gwamna Mai Mala Buni ya rubuta, inda ya mayar wa da Gwamna Nasir El-Rufai kan zargin tsige shi a matsayin shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa.
Jaridar indaranka ta rawiato cewa a wata hira da gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce shugaban kasa ne ya bayar da umarnin tsige mai mala Buni, ya kuma bada Umarnin nada gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a Matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar APC.
Sai dai kuma a wani da Buni ya rubuta, ya yi watsi da iƙirarin El-Rufai na cewa an tsige Buni a matsayin shugaban jam’iyyar.
Ɓangaren Buni ya yi ikirarin cewa kwamitin riko na jam’iyyar APC bisa doka ya mika al’amuran jam’iyyar ga Gwamna Abubakar Sani Bello kafin ya bar ƙasar nan zuwa Kasar Dubai domin duba lafiyarsa.
A cikin wasika mai dauke da kwanan watan 28 ga watan Fabrairu, Buni ya umurci gwamna Bello da ya rike mukamin Slshugabancin jam’iyyar lokacin da baya nan.
Ɓangaren na Buni, ya ƙara da cewa an tura wa Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, kwafin wasikar da kuma duk mambobin kwamitin rikon jam’iyyar, in ji jaridar The Nation, wacce ta ga wasiƙar.
Wani hadimi ga Buni, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce: ba wani ko wata kungiyar gwamnoni da take da ikon Buni Saboda a cikin wasikar sa ya bi doka wajen mika ragamar jam’iyyar ga Abubakar Sani Bello.
“Ya kamata gwamna El-Rufai ya gaya wa ‘yan Najeriya hakikanin abin da ya faru tsakanin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni a ranar Lahadin da ta gabata, Inda yace bayanansa akwai kuskure a cikin su.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi Bello da ‘yan CECPC ko irin wannan wasika ta zo musu daga Mai Mala Buni ?.” in ji hadimin na sa.