News
Bakano ya zama sabon shugaban ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kamar yadda kafar BBC Hausa ta bayyana, Malam Injiniya Mustafa Balarabe, wanda shi ne daga hannun dama a wannan hoto, sanye da rigar kwat, shi ne ya zama sabon shugaban wannan babbar ƙungiya, wato Ƙungiyar Injiniyoyi ta Duniya (World Federation of Engineers).
A kusa da shi, daga tsakiya, Jose Vieira ne, wanda shi kuma shi ne tsohon shugaban da Injinya zai karɓa daga hannunsa.
Na ɓarin hannun hagun kuwa shi ma wani babban Injiniya ne, mai suna Injijiya Malam Tasi’u Wudil.
TDR Hausa tana musu fatan alheri, da fatan hakan ya zamewa Kano da Najeriya wata sanadiyyar alheri.