News
Obaseki ba zai bar PDP ba, in ji Ayu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugaban Jam’iyar PDP na Ƙasa, Dakta Iyorcha Ayu, ya ce Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya na nan a jam’iyar kuma ba zai fita ba kamar yadda a ke raɗe-raɗi.
Ayu ya bada tabbacin ne a a Benin a jiya Alhamis a wani taron gangami Na goyon baya da a gwamnatin Edo shirya, inda ya ce Obaseki kadara ne ga PDP.
Ya ce da yawa da su ka bar PDP sun fara dawo wa kuma da yawa suna nan su na shirin dawo wa.
Shugaban ya kuma yin alƙawarin sasanta rikice-rikicen da su ka dabaibaye PDP a jihar cikin gaggawa.
A cewar Ayu da ga mako mai zuwa, mutane za su fara ganin abin da uwar jam’iyar PDP za ta yi wajen sasanta rigingimun da ke cikin jam’iyar a Jihar Edo.