News
arashin litar man jirgin sama ya tashi daga N190 zuwa N670 a makonni 2
Daga sani abbas sani
Kamfanonin jiragen sama a Nijeriya sun koka cewa farashin man jirgin sama ya yi tashin gwauron zabi da ga N190 zuwa N670 a kowacce lita ɗaya a cikin makonni biyu.
Kamfanonin sun kuma yi zargin karkatar da man zuwa kasuwar bayan-fage da wasu masu kawo man jirgin sama samfurin Jet A1 ke yi, wanda hakan ya sa farashin ya tashi ya kuma haifar da karancin sa.
Kazalika kamfanonin sun nuna damuwarsu kan yiwuwar karyewar kamfanonin jiragen sama a Najeriya, inda su ka kara da cewa sun damu matuka dangane da ci gaba da ƙarin farashin man jiragen.
Masu kamfanonin sun bayyana haka ne a yayin zaman kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken karancin man jiragen sama.
Allen Onyema, Shugaban Kamfanin Air Peace, ya ce a cikin makonni biyu farashin man jiragen ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 670.
Onyema ya ce ba don kakar siyasa ta zo ba, da kuma ganin cewa wannan gwamnatin na tallafa wa ɓangaren sufurin jirgin sama, da tuni masu kamfanonin sun rufe kamfanonin US a ƙasar.
Ya ce ma’aikatan ba za su iya kai wa sa’o’i 72 masu zuwa ba a cikin wannan hali ba sabo da ɗumbin bashin da ke kan su, inda su ke fargabar kada hukumar kula da kadarorin Najeriya, AMCON ta rurrufe ofisoshin su.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
