Connect with us

News

Rikicin APC: INEC ta ƙi karɓar takardar gayyatar taro da Sani Bello ya rubuta mata

Published

on

Spread the love

Daga maryam bashir musa

 

 

Advertisement

 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta, INEC, ta ƙi karɓar takardar gayyatar taron shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa da shugaban riƙo na kwamitin riƙon jam’iyar, Gwamna Abubakar Sani Bello ya aike mata.

A takardar da INEC ɗin ta rubuta wa Sani Bello, mai ɗauke da kwanan watan 9 ga watan Maris da kuma sa hannun Sakatariya Rose Anthony, hukumar ta ce takardar da a ka aike mata babu sa hannun Shugaban riƙo, Mai Mala Buni da Sakataren riƙo, Sanata John Akpanudoedehe.

Advertisement

A cewar INEC, hakan ya saɓa da sashi na 1.1.3 na kundin dokoki da tsare-tsaren gudanar da harkokin jam’iyyu na 2018.

Haka-zalika INEC ta kuma tunasar da wadanda su ka rubuta wasiƙar sashi na 82(1) na dokar zaɓe ta 2022.

INEC ta yi ƙarin bayani cewa sashin ya ce a na son jam’iyya ta bada sanarwar taruka ko ganawa da a ka shirya domin zaɓen shugabanni da kuma fitar da ƴan takara ‘a ƙalla kwanaki 2’ kafin lokacin.

Advertisement

Da ga bisani, INEC ta hori APC da ta riƙa kula da wasu muhimman batutuwa ta kuma riƙa aiwatar da su bisa kan bin doka da tsari.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *