News
Yan Bindiga Sun Sace Mutum 14 Suna Sallah A Masallaci A Giwa.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Yan bindiga sun kai hari wani masallaci da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, inda suka sace mutum 14 suna tsaka da sallah.
Rahotanni sun ce maharan sun mamayi masallacin ne da ke kauyen Tudun Amada, a daidai lokacin da mutanen suke sallar Isha.
A cewar wani mazaunin yankin, “Sun mamaye masallacin ne inda suke yi awon gaba da mutum 14. Sun kuma yi awon gaba da shanu da dama.”
Bayanai dai sun ce tsawon lokaci maharan suna yunkurin kai wa kauyen hari amma ba su samu dama ba, saboda ’yan sa-kan yankin sun hana su sukuni, sai a wannan karon.
Shi ma wani mazaunin yankin, ya ce, “’Yan bindigar sun raba kansu gida biyu; wasu suna masallacin, wasu kuma suna shiga gida-gida, inda suka sace mata sama da 10.
Wasu kuma suna ta kokarin kwasar daruruwan dabbobi kamar shanu da tumaki da awaki.”
Wakilinmu ya gano cewa ya zuwa yammacin Juma’a, mutum hudu daga cikin wadanda aka sace din sun samu kubuta daga hannun maharan.