Connect with us

Entertainment

awaƙa Angélique Kidjo da Black Coffee sun sami lambobin yabo a bikin Grammys

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

Mawaƙiya Angélique Kidjo ƴar Benin da mawaƙi Black Coffee ɗan Afirka ta Kudu sun sami lambobin yabo a bikin Grammy Awards na bana.

Kidjo ta sami lambar yabo a rukunin kundin waƙar da yafi yin fice a duniya mai suna Mother Nature. Akwai wasu mawaƙa uku yan Najeriya – Burna Boy, Yemi Alade da Mr Eazi.

Mawakiyar mai shekara 61 ta doke Wizkid da Femi Kuti da Rocky Dawuni dan kasar Ghana wadanda suka fafata da ita. Wannan ne karo na biyar tana lashe lambar yabo ta Grammys.

Advertisement

Shi kuma Black Coffee dan Afirka ta Kudu ya sami lambar yabo a rukunin kundin kidan rawa na zamani. Sunan kundin ‘Subconsciously album’.

Wannan ne karonsa na farko na samun lambar yabo ta Grammys. Ɗansa ya raka shi yayin da ya karbi lambar yabon, kamar yadda ake iya gabi a bidiyon da aka wallafa a Twitter.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending