News
Yan fashi sun Kai hari Wani gidan radio a I ada
Yan fashi sun kai hari gidan radio a na tsaka da shiri na kai-tsaye a Ibadan
Ƴan fashi sun kai hari kan wani gidan radio mai zaman kansa mai suna Fresh FM a safiyar yau Lahadi.
Rahotanni sun baiyana cewa a na tsaka da wani shiri na kai-tsaye sai ƴan fashin su ka kutso kai, inda su ka yi awon-gaba da na’ura mai ƙwaƙwalwa, wayoyi da sauran kayayyakin ma’aikata.
Wani maaikacin gidan rediyon ya shaida wa jaridar Punch cewa ƴan fashin sun kai harin ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
Ya ce basu taɓa kowa ba, amma sun tafi da kayaiyakin ma’aikata.
Sai dai kuma jaridar ta ƙara da cewa ba ta samu damar magana da kakakin rundunar ƴan sanda ta Jihar Oyo, Adewale Osifeso ba saboda wayar shi ba ta shiga lokacin da a ka kira shi kafin haɗa rahoton.
Advertisements
