Connect with us

News

Ya kamata shugaba Buhari ya bude ma’aikatar kula da biyan kudin fansa -Bulama Bukarti

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Shahararren lauya kuma me sharhi akan al’amuran tsaro, Bulama Bukarti ya ce ya kamata shugaba Buhari ya bude ma’aikatar kuda da biyan ‘yan Bindiga kudin fansa.

Ya bayyana hakane yayin da yake takaicin biyan ‘yan Bindiga kudin fansa har Miliyan 100 kamin suka saki shugaban bankin Manoma, Alwan Ali-Hassan.

Bulama Bukarti ya bayyana hakane ta shafinsa na Twitter.

Advertisement

Hakazalika

Ƴan fashin daji sun yi garkuwa da mata da ƴar Kwamishina a Plateau

Wasu ƴan fashin daji, ɗauke da muggan makamai, sun yi garkuwa da mai-ɗaki da kuma ƴar Kwamishinan Muhalli na Jihar Plateau, Usman Bamaiyi.

Jaridar The Nation ta biyo cewa ƴan bindigar sun kutsa kai gidan Kwamishinan da ke Unguwar Gindiri a Jos, inda su ka yi awon-gaba da matar sa da kuma ƴarsa.

The Nation ta ce kakakin rundunar ƴan sanda ta Jihar Plateau, ASP Gabriel Ogaba ya tabbatar da harin.

Ya ce rundunar ƴan sandan jihar ta na da masaniya a kan harin kuma tuni ta tashi tsaye wajen bin diddigin ƴan fashin dajin domin kuɓutar da waɗanda su ka ɗauke.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending