News
Wasu Matasa sun kashe wani Yaro Akan Mangaro a wani Kauye dake gombe
Daga yasir sani abdullahi
Da safiyar yau Wasu matasa Yan kauyen Jauro sule dake Yankin kalshingi ward, a karamar Hukumar Akko, dake jihar Gombe suka kashe wani Yaro Dan kauyen Lariye (Gendeji) a cikin shingen su na Mangaro.
Yaron wanda suke da mallakin mangaro ana kyautata zaton Yayi sammako domin tsintar wadanda suka fado kafin Dabbobi su rigashi shine wadancan matasan suka farmasa suka kashe shi.
Zuwa Yanzu jami’an Yan sanda sunje kauyen yayin Bincike inda wasu Yara suka bada Tabbacin cewa Yan Kauyen jauro sule sukayi kisan bisa hujjar cewa suna hango su kafin suyi kisan.
Jami’an Yan sandan da suka shiga Lamarin sun bada Tabbacin Yin kwakkwauran Bincike tare da hukunta duk wanda suka kama Da Laifi akan Wannan mummunan Aikin.
Advertisements
