Connect with us

News

Good Friday: Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranar hutu

Published

on

Daga maryam bashir musa

 

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 15 da Litinin 18 ga Afrilu, 2022, domin gudanar da bukukuwan good Friday da kuma Easter Monday na bana.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Shu’aib Belgore ya fitar a madadin ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola.

Cikin sanarwar Aregbesola ya buƙaci Kiristoci da su yi koyi da halayen sadaukarwa, haɗin kai, gafara, alheri, soyayya, zaman lafiya da haƙuri, irin na Yesu Kiristi.

Don haka ya yi kira ga Kiristoci da sauran ƴan Najeriya da su yi amfani da bikin Easter na bana wajen yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wani kalubalen tsaro da ke addabar kowane ɓangare na ƙasar nan.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending