Connect with us

News

Ƴan Najeriya na Shan Baƙar Wahala a ƙarƙashin Gwamnatin Yanzu -Inji Sheikh Gumi

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana rashin jindaɗi na yadda Matsalar Tattalin Arziki da na tsaro ke cigaba da addabar Kasar.

Gumi, wanda ya kasance tsohon Soja, ya jaddada irin yadda ƴan Najeriya ke cigaba da shan wahala sakamakon waɗannan matsaloli a Ƙasar.

Advertisement

A wata tattaunawa da Majiyar mu a ranar Talata, Gumi ya koka na yadda ƴan Najeriya da yawa basa iya ciyar da kansu a yayinda Farashin Kayayyaki ke cigaba da tashin gwauron zabi a Kasuwanni.

Dayake jawabi akan kai harin Jirgin Ƙasa na Abuja-Kaduna, Malamin Musuluncin ya addu’ar gaggawar sakin waɗanda ake riƙe dasu a wajen ƴan bindiga.

Advertisement

Gumi yayi kira ga ƴan Najeriya dasu zama masu haɗin kai a yayin da Babban Zaɓen 2023, ke cigaba da matsowa, domin samar da ingantacciyar Gwamnati da zata magance wahalhalun da ƴan Najeriya suke sha a ƙarƙashin wannan Gwamnatin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending