Connect with us

News

Muna kashe miliyan 30 don siyan man diesel– Asibitin Aminu Kano

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

Hukumomin asibitin koyarwa na Aminu Kano sun tabbatar da karin kudin ganin likita da gwaje-gwaje da ma sauran aikace-aikacen da ake yiwa marasa lafiya a Asibitin.

Advertisement

Mai magana da yawun asibitin Hajiya Hauwa Abdullahi ta tabbatar da karin kudin da akai yayin tattaunawar ta da Premier Radio.

Asibitin Aminu Kano ya kara kudin ganin likita da kudin wasu aikace aikace a asibitin.
Ta ce karin kudin ya farune sakamakon dalilai da dama da suka hadar da rashin wutar lantarki da kuma tsadar man Diesel.

Advertisement

Ta kara da cewa karin ya zama dole kasancewar asibitin zai iya durkushewa baki daya tana mai cewa asibitin yana kashe sama da miliyan 30 wajen siyan disel a kowane wata.

Hauwa Abdullahi tace asibitin yana kashe wannan kudi ne kasancewar akwai bukatar wutar lantarki ta awanni ashirin da hudu a asibitin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending