Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekaru mai wakiltan Kano Central ya ki amsa gayyatar gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na zuwa Abuja ganin Shugaba Buhari, bayan gayyatar da Ganduje ya mika masa har gidansa a daren ranar Juma’a da nufin su tafi Abuja ganin Buhari game da fitarsa daga APC.

Wasu na kusa da Shekarau sun ce da farko ya yi niyyar tafiya Abujan amma sai ya gano cewa Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, da wasu gwamnoni ne ke son ganawa da shi ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Idan baku manta ba, Nasara Radio ta kawo muku rahoton da Daily Trust ta fitar, cewa an mika wa Shekarau gayyatar ne ta hannun gwamna Ganduje, inda wasu fusatattun matasa suka yi masa ihu a lokacin da ya ziyarci gidan Shekarau da ke Mundubawa domin shawo kansa ya bi shi su shiga jirgin sama su tafi ganin shugaban kasa a Abuja misalin karfe 1 na daren Asabar.

Advertisement

Abin da yasa Shekarau ya fasa zuwa Abujan Duk da cewa da farko Shekarau ya amince zai tafi Abujan, wasu na kusa da shi sun shaida wa Daily Nigerian cewa Shekarau ya fasa tafiyar ne bayan ya gano ba shugaban kasar bane ke son ganinsa amma shugaban APC, Abdullahi Adamu da wasu gwamnoni ne.

Ba a samu Mallam Shekarau ba a wayansa tun bayan da ya kammala shirin koma wa jam’iyyar NNPP. Don haka suna kokarin tafiya da shi Abuja domin su shawo kansa ya fasa komawa NNPP.

Advertisement

“Sun san cewa Mallam yana girmama shugabanni, kuma ba zai ki amsa kirar shugaban kasa ba. Wannan shine dalilin da yasa suke yi wannan dabarar.

“Amma maganan gaskiya shine Mallam ya kai matakin da ba zai canja shawararsa ba. Idan ya koma APC, ina tabbatar maka kashi 80 cikin 100 na magoya bayansa za su koma NNPP.

Advertisement

“Kuma ko sun bashi tikitin takara ba tare da hamayya ba, ba zai iya cin zabe ba a APC,” a cewar majiyar