News
Mutumin da ya shafe shekara 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba ya rasu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Allah Ya yi wa mutumin da ya shafe shekara 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba Sheikh Muhammad bin Abdul-Wahhab Aal Ash-Sheikh rasuwa.
Sheikh Muhammad ya rasu ne a yau Laraba, 25 ga watan Mayu wanda ya yi daidai da 24 ga watan Shawwal a wani asibiti a birnin Jiidah na Saudiyya.
Yana daga cikin mutanen da suka samu albarkar yin sallah a bayan limaman Masallacin Harami, kuma ya shafe shekara 70 yana yin hakan.
Ana yawan ganinsa a bidiyo a bayan limaman a cikin shekara 10 da suka wuce.
– BBC
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
