News
Kisan Harira: ’Yan IPOB Za Su Dandana Kudarsu — Buhari
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da ’yan haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB suka yi wata ’yar Arewa mai suna Harira da ’ya’yanta su hudu a Jihar Anambra.
Mutumin da ya shafe shekara 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba ya rasu
Shugaban ya bayyana kisan nata da ma na sauran mutane da kungiyar ke ci gaba da yi a yankin a matsayin dabbanci, inda ya ce za su dandana kudarsu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shi, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, Buhari ya gargadesu cewa su jira tsattsauran mataki daga jami’an tsaro.
Buhari ya kuma yi gargadi a kan daukar kowanne irin mataki na ramuwar gayya daga kowane bangare na kasar nan.
Ya ce yanzu haka, jami’an tsaro na bincike kan sahihanci da gaskiyar hotuna masu tayar da hankali da ake yadawa a kan kisan.
Sanarwar ta kuma gargadi ’yan Najeriya da su guji gaggawar yanke hukunci ko daukar duk wani matakin da zai dada dagula al’amura, inda ya ce kamata ya yi a kyale doka ta yi aikinta.
Buhari ya kuma gargadi jama’a kan ci gaba da yada hotunan musamman a kafafen sada zumunta domin su ba masu yunkurin raba kan kasa kunya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
