Connect with us

News

Sama da Naira Miliyan 20 kowane Delegates din PDP dake zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa ya samu

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

Rahotanni sun bayyana cewa, akalla kowane Delegates na PDP dake zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a Abuja ya samu dala 50,000.

Wadannan kudi a Naira sun kai kimanun Naira Miliyan 8.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa, Gwamna Wike na raba dala $15,000, sai kuma Atiku Abubakar dake raba dala 20,000, sai Saraki dake raba dala $10,000, sai kuma Tambuwal da shima yake raba dala $10,000.

Advertisement

Hajazalika

Na ga sai wasa da kudi ake ni kuma ba zan iyaba dan haka na hakura da takarar

-Inji dan takarar shugaban kasa na PDP, Hayatu

Me neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Muhammad Hayatudeen ya janye daga takarar.

Ya bayyana hakane a wasikar da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDPn yayin da ya rage saura awanni kadan a fara zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Muhammad Hayatudeen ya bayyana cewa, yaga gaba daya sai wasa ake da kudi yayin da shi kuma ba zai iya yin hakan ba ahiyasa ya janye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending