Connect with us

News

Yakamata Gwamnati ta Samar da makarantun manya ( Adult Education ) da makarantun gaba da sakandire(Tatiary School) a gidan gyaran hali- Comr Abba Alra-iwas

Published

on

Yakamata Gwamnati ta Samar da makarantun manya ( Adult Education ) da makarantun gaba da sakandire(Tatiary School) a gidan gyaran hali.

*Yakamata Gwamnati ta Samar da makarantun manya ( Adult Education ) da makarantun gaba da sakandire(Tatiary School) a gidan gyaran hali*.
Yakamata Gwamnati ta Samar da makarantun Saboda Samarwa da Al, umma cigaba musammam ma wadanda kaddara ko azal ta afka mu su a rayuwa ma su shiga gidan gyaran hali.
Samar da makarantun manya (Adult Education) zai kara taimakawa wajen dakile kananun laifunfuka a wani bangaren ma harma da manyan laifunfukan, sannan Kuma yin hakan kamar an Samar mu su da makoma ne a rayuwa Saboda mutane da dama su na aikata laifunfukan ne batare da sun san hukuncin laifin ba.

Haka zalika wa su Kuma su na futowa daga gidan gyaran hali batare da sun san inda su ka dosaba sakamokon rasa mafarkan su da su kai wa sun su kuma su na futowa za su kara aikata wani laifin za,akara mai da su gidan, su na karar da rayuwar su gaba daya batare da Amfanar da kan su komai ba ballatana kuma su Amfanar da kasar su.

Amma ba su ilimi a gidan tare da ba su shedar kammala sakandire (Certificate) hakn kara mu su nutsuwa da ya kuma ba su saiti a rayuwa domin kowanan su zai san kan sa hakan kuma zai sa su dinga nemawa kan su abin yi da wannan takardun makarantar kuma ilimin su bazai bar su su dinga aikata wani laifin da zai dawo da su gidan ba Saboda kowane Dan Adam yana san rayuwa mai dadi.

Su kuma makarantun gaba da sakandire (Tatiary School) amfani su akwai wadanda su ke da shedar kammala sakandire ( o, level ) kuma kaddara take kawo su gidan har su kai wani tsawon lokaci mai tsayi a gidan ba su futaba wanda hakan yana sa su rasa abun da su ke so su cimma a rayuwar su, Amma idan har akwai makarantun to za su samu damar cigaba da karatun su kamar DIPLOMA/ NATIONAL DIPLOMA KO HIGH NATIONAL DIPLOMA.
Kuma duk Wanda ya futo daga gidan zai futone tare da kudirin wani abu dayake so yacimma a rayuwar sa , muddin Gwamnati za ta samar da wadannan makarantun a gidan gyaran hali to za ta kawar da abubuwa da yawa a cikin Al, umma kuma ta Samar da cigaba Mai dorewa.

Comr Abba Alra-iwas
Shugaban kungiyar organization for union Peace and Assistance ( U P A )

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending