Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Atiku Abubakar murnar nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP babbar jam’iyyar hamayya.
Tinubu kuma ya bayyana fatansa na kasancewa abokin hamayyar Atiku a zaɓen 2023.
A ranar Asabar PDP ta zaɓi Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. Atiku shi ya fafata da Buhari a zaɓen 2019.
Tinubu, duk da ya yaba da yadda jam’iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da gwaninta a ranar Asabar, amma ya ce jam’iyyar na da ƙalubale a gabanta domin har yanzu a cewarsa ƴan Najeriya ba su manta da ɓarnar da ta yi ba a shekaru 16 da ta yi tana mulki.
