News
Delegate ya rabe milyoyin kuɗaɗen da ya samo a zaɓen fitar da gwanin PDP
Wani delegate na PDP wanda ya samu kuɗi sosai a lokacin zaɓen fitar da gwani ya raba kuɗin tsakanin al’umomin karamar hukumarsa ta Sanga a Jihar Kaduna.
Mutumin mai suna Tanko Rossi Sabo, ya wallafa a shafinsa na Facebook yada ya gabatar da kuɗin naira miliyan 12 domin a rabawa maɓukata a karamar hukumarsa.
Daga cikin abubuwan da aka yi da kuɗin akwai sayen rigunan jerseys da biyan kuɗin makaranta da asibiti ga mutane. Ya kuma raba sauran kuɗaɗen ga magoya bayansa.
DA ƊUMI-ƊUMI: Gidan man AA Rano ya kama da wuta a Kano
Mista Tanko ya ce ko wacce irin muhawara ko suka da za a tafka bai dame shi ba, tunda dai duk abin da ya samo ya dawo gida ya sanya farin ciki a fuskokin al’ummarsa.
Tanko Rossi na cikin delegates din Kaduna da suka halarci taron PDP na kasa inda aka gudanar da zabe da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a PDP.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
