Connect with us

News

Zaben 2023: Shin farin-jini a shafukan sada zumunta na tasiri a lokacin zaɓe?

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Jama’a da dama, musamman a shafukan sada zumunta a Najeriya, suna ci gaba da bayyana mamakinsu game da kayen da wasu da suka yi fice a shafukan sada zumunta suka sha a zabukan fitar da gwanin da aka gudanar a jam’iyyu daban-daban.

Sai dai masana harkokin siyasar kasar na ganin wannan ba abin mamaki ba ne ga waɗanda suka san siyasa da yadda ake yin ta – daga sama har ƙasa.

Advertisement

Sun bayyana cewa ko da yake shafukan sada zumunta, irin su Facebook da Twitter da makamantansu, suna taka muhimmiyar rawa wurin tallata ƴan takara da bunkasa siyasa sai dai a Najeriya wasu na zuzuta tasirin su.

Akwai wasu mutane da suka yi fice a shafukan sada zumunta waɗanda idan suka ce tak, sai ka ga dimbin mutane sun yi tsokaci a ƙasan abin da suka rubuta a shafukansu na sada zumunta, wanda hakan yake sa wasu mutane suke ganin za su iya yin tasiri a zaɓuka.

Advertisement

Abin da mutane da dama ba su fahimta ba shi ne, galibin mabiyan wadannan mutane na shafukan sada zumunta sun fito ne daga yankuna daban-daban na kasar, wasu ma ba a Najeriya suke ba, don haka ba za su yi tasiri kan zabukan da wadannan ‘yan siyasa na shafukan sada zumunta za su fafata a ciki ba.

Alal misali, idan akwai ɗan siyasa a jihar Filato da ke da mabiya miliyan guda a shafin Facebook, kada mutane su ɗauka mutum miliyan guda ɗin nan gaba ɗaya ƴan jihar Filato ne domin zai iya kasancewa akwai wasu daga Kaduna da Legas da Kogi da kasar Faransa da sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending