News
Naziru sarkin Waka ya zabi gawuna gwaninsa da zai wake. zaben: 2023
Daga Yasir sani. Abdullahi A yayin da babban mawakin siyasar Nigeria dama wasu kashen Africa dauda kahutu rarara ya dauki gwanin da da zai wake a zaben 2023 wato hon Sha,ban Ibrahim sharada
Shima dai angano tsohon sarkin Waka Mai murabus Wanda akafi sani da naziru sarkin Waka ya fitar da hotunansu dashi da Dr Nasir Yusuf gawuna
Hon,Sha,ban Ibrahim sharada shine Dan takarar gwamnan jahar kano a jamiyyar ADP shikuma Dr Nasir Yusuf gawuna ke zama Dan takarar gwamnan jahar kano a jam,iyyar APC
Mafi akasarin na ra,ayoyin Jama,a dai nata Cece. Kuce na yadda akaga mawakin jam,iyyar APC dauda kahutu rarara ya dauki wata jam,iyya daban da zai wake sabanin jam,iyyar APC a zaben kano dake karatowa
Kuma mutane nata ganin tsakanin mawakin rara da Sha,ban sharada kamar akwai wata tsama a tsakanin su tunda daga lokacin da Sha,ban din ya barranta kansa da gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar ganduje yabi tsagin G7
Shima dai naziru sarkin Waka ana ganin kamar bai taba wake mataimakin gwamnan ba Dr Nasir Yusuf gawuna ba Amma Shima haryanu bai bayyana aniyar sa ta komawa tsagin mataimakin gwamnan ba Amma cikin hotan naziru sarkin Wakan da Dr yasuf gawuna sarkin Waka yayi rubutu Yana Mai cewa wannan shine zama na farko da sukayi dashi
Amma dai za,mu ajiye Karin maganar da bahaushe ke cewa idan kaga kare na shinshinar takalmin to da alama dauka zai,Yi
