News
Sojojin Najeriya sun kaddamar da bincike kan kisan Goni Aisami
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike kan kisan da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ta biyu ta Operation Hadin Kai, Kennedy Anyawu, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Damaturu.
Rundunar ta ce tuni ta kama sojoji biyu, kofur John Gabriel da kofur Adamu Gideon a kan batun kisan malamin.
Rundunar da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ne za su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kazalika rundunar ta kuma kafa wani kwamiti da zai bankado yadda lamarin ya auku.
Idan aka kammala bincike aka gano wadanda suka aikata kisan to lallai za su fuskanci hukunci da ya kamata in ji rundunar.
Kisan malamin ɗan Jihar Yobe ya ja hankalin ‘yan ƙasar musamman ma’abota shafukan zumunta.
A ranar Juma’ar da ta wuce ne aka kashe malamin a lokacin da yake tuƙa motarsa a kan hanyar zuwa Gashua daga Nguru.
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News21 hours ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
