News
Keir Starmer Ya Yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya
Firaministan Birtaniya Kier Starmer ya sanar da murabus daga muƙaminsa, kodayake ya ce zai ci gaba da zama kan kujerar har zuwa lokacin da jam’iyyar Labour za ta yi zaɓen sabon jagora wanda zai zama magajinsa.
Da safiyar yau Litinin ne Starmer ya sanar da wannan mataki yayin wani taro da ya kira a harabar Downing Street, gaban idon manyan muƙarraban gwamnatinsa tare da manema labarai.
Wasu Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna
Cikin jawabinsa, Firaministan na Birtaniya mai murabus, ya ce nan da watan Satumba ne za a gudanar da zaɓen sabon jagora don jan ragamar ƙasar, sai dai kafin nan zai ci gaba da aiki a matsayin mai barin gado.
Cikin yanayi na shessheƙar kuka ne Keir Starmer ya tabbatar da wannan murabus inda ya ce zai haƙura da kowanne aiki tare da mayar da hankali wajen baiwa kyakkyawar matar shi da yaranshi kulawar da ta kamata.
Murabus ɗin na Starmer kai tsaye ya buɗe ƙofa ga Firaminista na 7 cikin shekaru 10 a ƙasar, wadda ta faɗa cikin rikicin siyasa tun bayan ficewa daga ƙungiyar Tarayyar Turai.
Tsawon watanni Starmer ya shafe yana fuskantar matsin lamba tare da neman murabus ɗinsa, sai dai lamarin ya fi tsananta a yanzu tun bayan da Andy Burnham ya lashe zaɓe tare da dawowa Westminster.
Ƙasa da shekaru 2 baya ne Starmer ya lashe zaɓen ƙasar tare da alwashin daidaita matsalolin siyasar da suka dabaibaye ƙasar.
