Connect with us

News

Mutum fiye da 25,000 ne suka ɓace a Najeriya saboda rikici – ICRC

Published

on

Nigerian

Daga: Muhammad Muhammad zahraddin

Ƙungiyar agaji ta duniya, ICRC ta ce fiye da mutum 25,000 ne suka yi ɓatan dabo a Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Shugaban tawagar ICRC, Yann Bonzon ya ce adadin kari ne kan rahotannin ɓatan mutane sama da 2,000 da suka samu bayan Janairun 2021.

Ya yi magana ne a wajen wani taro a Abuja, babban birnin ƙasar domin bikin ranar tunawa da mutanen da suka ɓace ta bana.

Bonzon ya bayyana cewa fiye da rabin mutanen da suka ɓata yara ne da yawansu ya kai sama da kashi 50 cikin 100 na adadin.

Ya ce mata su ne na biyu a yawan mutanen da ba a san inda suke ba. Sai dai ya ce adadin da aka bayar bai kai na waɗanda suka bace a Najeriya ba tare da an kai rahoto ga hukumomi ba.

Advertisement

A cewarsa, rashin tattara bayanai da kuma mayar da hankali sune manyan ƙalubalen rashin adana bayanai na mutanen da suka yi ɓatan dabo.

An shafe shekara 13 ana fama da rikicin Boko Haram da aka soma a jihar Borno kuma ya yaɗu zuwa wasu jihohin kamar Yobe da Adamawa. Ɗalibai da mata sun shiga komar ƴan bindiga.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending