News
Rundunar sojojin nigeria tayi nasarar kashe babban Dan fashi Daji tare da kame wasu guda Uku
Daga yasir sani Abdullahi
Rundunar Sojin Nigeria sunyi nasarar kashe Wani Dan ta,adda Daya 1 tare da kame wasu guda uku a jahar Kaduna
Jaridar daily nigerian Hausa ta rawai to cewa Dakarun runduna ta 1 ta Rundunar Sojojin Ƙasa sun kashe wani dan fashin daji tare da cafke wasu guda uku da ake zargi a Kaduna a jiya Litinin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Talata a Kaduna.
A cewar sanarwar, sojojin sintiri na yaki, ƙarƙashin jagorancin babban kwamandan rundunar, GOC, shiyya ta ɗaya ta sojojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, tare da tawagar kwamandojin aiki ne su ka samu nasarar kama ƴan ta’addan.
“Jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga a garuruwan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da kuma Dogon Dawa a jihar Kaduna, yayin da suke sintiri a jiya Litinin.
lokacin da ake musayar wuta a ana gudanar da aikin, rundunar ƴan sintiri ta yi galaba a kan ƴan bindigar da karfin wuta, inda suka kashe daya daga cikinsu, yayin da aka kama wasu uku da ransu, sannan wasu daga cikin ƴan ta’addan suka tsere da raunukan harbin bindiga Nwachukwu ya ce rundunar ta kuma kwato bindiga kirar AK 47 guda daya, harsashi na musamman mai girman 7.62 mm 7.62 da kuma babura 18.
A nata jawabin rundunar Yan Sanda ta 1 tace tana duk Mai yiwuwar domin kawo Karshen Yan ta,adda
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
