Gwamnatin Brazil ta ce ta hana sayar da wayoyin iPhone wadanda ba su da caja a kasar.
A wata sanarwa da ma’aikatar shari’ar kasar ta fitar, ta ce ta ci tarar kamfanin wayoyin fam miliyan 2.04
Da Dumi-Duminsa: Ma’aikatan Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Sun Dakatar Da Aiki
Hukumar kula da hakkin mai saye ta kasar ta ce matakin da kamfanin Apple – wanda ke kera wayoyin – ya dauka na rashin sayar da wayoyin tare da cajarsu ya ci karo da hakkin masu saya.
To amma kamfanin na Apple ya ce zai daukaka kara game da wannan matakin.
