News
Da Dumi-Duminsa: Ma’aikatan Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Sun Dakatar Da Aiki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An kawo cikas a harkokin zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Mallam Aminu Kano (MAKIA) sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NAMA.
Yawan Ciwo Basussuka: Gode mana yakamata a yi, ba yawan ƙorafi ba – Buhari
Solacebase ta ruwaito cewa jiragen da zasu tashi daga Kano a safiyar yau litinin sun samu cikas yayin da jami’an kula da zirga-zirgar jiragen suka dakatar da ayyukansu wanda ya shafi sauka da tashin jirage.
An hana jiragen sama irin su AZMAN da Max Air da aka shirya zuwa Abuja da Legas su tashi.
Daga baya an ce fasinjojin da suka shiga jirgin su sauka yayin da jami’an kula da zirga-zirgar jiragen suka rufe ayyukansu.
An sanar da Solacebase cewa kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NATCA ta rufe ayyukan zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen MAKIA kan samar da wutar lantarki ga cibiyoyin NAMA da ma’aikatan da aka katse.
Wata majiya a filin jirgin ta shaida wa Solacebase cewa wasu muhimman mutane da suka makale a filin jirgin da suka hada da wasu ‘yan majalisar tarayya, mataimakan gwamnoni da sauran su tuni suka shiga tsakani domin warware sabanin da ke tsakaninsu ta yadda za a maido da aikin jiragen.
