Connect with us

News

Za’ayita Ta ƙare Ahmed Lawan da Bashir Machina

Published

on

Lawan Ahamed Bashir Machina

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu babban birnin jihar Yobe ta sanya ranar Laraba 28 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan rikicin takarar Sanatan jam’iyyar APC na arewacin jihar Yobe wanda aka shafe watanni ana tataburza tsakanin shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmad Lawan da Bashir Shariff Machina.

Advertisement

Kafin hakan dai Bashir Machina ne ya lashe zaben fidda gwanin a wani zaben fidda gwani daya fafata shi kadai.

Dukdacewa akwai ƴan takara uku da suka yanki Fom amma aka hana su fafatawa a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Advertisement

Mai shari’a Fadima Aminu ta sanya wannan ranar ne domin kawo karshen wannan shari’ar kafin lokaci ya kure.

Kafin hakan dai a wani zama da aka gudanar a makon jiya Mai Shari’ar ta saurari zazzafar muhawara tsakanin lauyoyin mai kara (Bashir Machina) da wadanda ake kara (Ahmed Lawan,APC da INEC)

Advertisement

Jibi dai, za’ayi ta takare dukdacewa akwai damar daukaka kara ga wanda hukunci baiyi masa daɗi ba

Muhimman abubuwan da Ahmed Lawan ya dogara akai.

Advertisement

1. Ahmad Lawan yasamu goyan shugabancin jam’iyyar APC ta jihar Yobe.

2. Lawan ya samu goyan bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu.

Advertisement

3. Lawan yana da goyan bayan dattawan jam’iyyar APC na kasa dana jihar Yobe.

4. Ahmed Lawan ya samu goyan goyan gwamnoni da kuma wasu daga cikin sanatoci.

Advertisement

5 Lawan a kwanaki baya INEC ta ayyana shi cikin wadanda zasu yiwa APC takarar saboda jam’iyyar APC tace ya yanki Fom ɗin Sanata.

6. Dokar zaɓe, tace Jam’iyyar siyasa ce take da ikon tura sunan ɗan takara ba INEC ba.

Advertisement

7. Sauran mutanen da suka yanki Fom din Sanatan Yobe ta Arewa suma sun soki sakamakon zaɓen da Bashir Machina yake tunkaho da shi.

8.Bashir Machina shi kadai ya gudanar da zaɓen fidda gwaninsa.

Advertisement

*Hujjojin da Bashir Machina ya dogara akai.

1. Ahmed Lawan bai fafata a zaben fidda gwani na Sanatan Yobe ta Arewa ba.

Advertisement

2. Ahmad Lawan bai yanki Form ɗin takarar Sanatan ba.

3. Lawan fom ɗin takarar shugabancin kasa ya mallaka, ya kuma sha kayi a hannun Tunubu.

Advertisement

4. Bashir Machina yana da goyan bayan INEC saboda wakilin su ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwani a watan Mayu.

5. Machina yana dauke da shaidar lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Advertisement

6. Lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu suna goyan bayan Machina.

7. Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC da mataimakin suna goyan bayan Machina, saboda Mai Mala Buni da Bashir Machina tsoffin yaran Tinubu ne a jam’iyyar AC.

Advertisement

8. Machina yanada goyan wani bangare na jam’iyyar APC Amma marasa ƙarfi.

#yobenorth
Yanzu dai zamu saka na mujiya muga Yanda zata kaya a ranar Laraba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending