News
Gawurtacciyar guguwa mai suna Iyan ta tagayyara sassan jihar Florida
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gawurtacciyar guguwa mai suna Ian hade da ruwan sama da iska mai karfin gaske na ci gaba da ɗaiɗaita sassan jihar Florida ta Amurka, baya ga haddasa ambaliya a yankunan gabar teku a kudu maso yammacin jihar.
Hotunan bidiyo da aka yada na nuna yadda ruwa ya mamaye biranen Naples da Fort Myers tare da shanye motoci da gidajen mutane.
Gwamnan Florida, Ron de Santis ya ce guguwar na ɗaya daga cikin guguwa biyar mafi karfi da suka taba auka wa Florida — an kuma tafka asara a kusan ko’ina a jihar.
Sai dai karfin mahaukaciyar guguwar ya ragu tun lokacin da ta dira a yankunan Florida, amma masu hasashe na cewa za ta iya haddasa mamakon ruwan sama a birnin.
BB
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
