News
Amurka za ta bai wa Ukraine karin makaman yaki ciki har da atilare na miliyoyin daloli
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Amurka ta sanar cewa za ta bai wa Ukraine karin tallafin kayan aikin sojoji na dala biliyan 1 da miliyan 100.
Tallafin dai zai kunshi karin makaman atilare na HIMARS — makaman da ake ganin su suka taimaka wajen nasarorin da Ukraine take samu a filin daga kan dakarun sojin Rasha a wannan lokaci.
Haka zalika za a ba su naurorin kakkabo jirage marasa matuka, da karin harsasai da na’urar hango makamai da motoci masu sulke.
Tallafin dai zai ba da damar ba da kwanturagin wadannan makamai, maimakon a debo makaman daga rumbun makaman Amurka, da kuma tsara yadda Ukraine za ta ci gajiyar makaman na tsawon lokaci.
BBC
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
