Connect with us

News

Kotu a Najeriya ta ba da umarnin a kamo wani dan Burtaniya

Published

on

Kotu

DAG MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umarnin kamo wani dan Burtaniya, James Nolan saboda ya keta sharuddan beli.

Advertisement

Mai shari’ah Ahmed Mohammed ne ya ba da umarnin bayan James Nolan wanda darakta ne a kamfanin Process and Industrial Development Limited (P&ID) ya gaza bayyana a gaban kotu.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta shigar da James kara tare da kamfanin Lurgi Consult Limited da sauran wasu, a wata shari’a da ta shafi halasta kudin haram kimanin dala biliyan 9.6.

Advertisement

Da yanke ba da hukunci, Mai shari’ah Ahmed Mohammed ya ce James ya karya sharuddan belin da kotu ta ba shi, don haka kotu ta soke belin kuma ta fitar da sammaci don a kamo shi, duk inda ya shiga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending