Connect with us

Kasuwanci

Saudi Arabia za ta fara kerawa da sayar da motoci masu aiki da lantarki a 2026

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

DAGA MUAHMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Ministan Sadarwa da Fasahar Bayanai na Saudiyya, Injiniya Abdullah Al-Swaha ya ce kasar za ta kera tare da fitar da motoci masu amfani da wutar lantarki sama da 150,000 a 2026.Babban kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki na Amurka Lucid Motors Company na son ya rika samar da motocin 150,000 a Saudiyyar a duk shekara, daga shekara ta 2027, kamar yadda ministan ya bayyana jiya Laraba.Tun da farko shugaban kamfanin Peter Rawlinson ya ce nan da wani dan lokaci suke son fara aikin kafa masana’antar a Saudi Arabia.

Dan Takarar Gwamna na PRP ya shiga Muhawarar Zaben Media Trust

Ya ce, “Muna son fara kera motocin a 2025 kuma za mu kara yawansu a 2026 da 2027 mu kai motoci 150,000 a duk shekara” Ministan zuba jari na Saudi Arabia, Khalid Al-Falih ya ce kamfanin ya fara gina ma’aikatarsa a kasar a watan Mayu na wannan shekara.

Ma’aikatar za ta kasance daya daga ciki guda uku na kamfanin mai cibiya a California, wanda Saudiyya za ta mallaki kashi 61 na hannun jarinsa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending