Business
Motocin Dangote 18 Makare Da Siminti Sun Sha Da Kyar A Hannun IPOB
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Motocin Kamfanin Dangote su 18 dauke da lodin siminti sun sha da kyar a hannun ’yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biyafara a Owerri, Jihar Imo.
Isa Minjirya, daya daga cikin direbobin motocin a hirarsa da Aminiya a ranar Litinin, ya ce, sun shiga tasku ganin motocin daukar kaya da aka kona.
Manyan motoci sun tare hanyar Abuja kan rufe masana’antar Dangote
Uba Ya Karya Hannun Jaririnsa Mai Wata 2 Saboda Kuka
A cewarsa, sun taso ne daga garin Ibese na Jihar Ogun a kan hanyarsu ta zuwa Fatakwal ranar Asabar, amma samun labarin da suka yi na kone manyan motocin ’yan Arewa, tsakanin Owerri zuwa Onitsha, sai suka yi hayar ’yan rakiya kuma ’yan gari wadanda za su bi da su ta wata hanyar daban.
Amma da shiga Abeokuta ta Jihar Ogun sai aka kama su, tare da kai su gidan gwamnati, bisa laifin bin hanyar da ba ta dace ba.
A gidan gwamnatin kwanan su biyu a tsare, amma saboda yawansu, sai gwamnati ta shiga yarjejeniya da kamfanin, daga karshe wani dan kasuwa a garin ya saye simintin baki dayansa.
A ranar Litinin, ake sa ran gama sauke lodin motocin 18, sannan su juya zuwa Fatakwal, sai dai bai san yadda za ta kasance ba kan hanyarsu ta komawa ba.
Kungiyar IPOB ta yi kaurin suna a wajen kai hare-hare da kisa a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da sunan fafutuka.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
