Connect with us

News

Buhari ya taya Sabon Shugaban Brazil murna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen taya sabon zababben shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva murnar lashe zaben da aka gudanar a kasar.

 

Advertisement

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce yana fatan sabon shugaban kasar zai karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

Elon Musk zai yi sauye-sauye a Twitter bayan sayen kamfanin

Advertisement

”Ina fatan yin aiki da sabon zababben shugaban kasar domin ci gaba da karfafa dankon zumuncin da alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashenmu”, in ji sanarawa.

 

Advertisement

Lula ya yi nasara da karamin jinjaye kan abokin hammayarsa Jair Bolsonaro wanda har yanzu bai amince da shan kaye ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending