News
Kamfanoni sun yi karin kuɗin ruwan leda a Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar masu samar da ruwan sha a roba ko leda a Najeriya sun sanar da anniyarsu ta karin kudin ruwa daga naira 200 jaka guda zuwa 300.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar Clementina Ativie ta fitar a Abuja.
Ta ce karin kudin na da alaka da hauhawar farashi a fanin kayayyakin da suke amfani da su da kuma yanayin tattalin arzikin kasar.
Atibie ta yi kira ga ‘yan Najeriya su yi hakuri sakamakon yanayin da wannan kari zai iya jefa su.
A watan Nuwamba 2021 aka yi karin kudin ruwan zuwa naira 200.
Advertisements
