News
APC ta Kano ta fara yakin neman zabe a Gaya LG
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A ranar Laraba ne jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a jihar Kano ta kaddamar da yakin neman zabenta a karamar hukumar Gaya.
Da yake jawabi a lokacin bikin, gwamna Abdullahi Ganduje, ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyar za ta samu nasara a dukkan matakai a zaben 2023 mai zuwa.
Kotu ta tabbatar da aishatu binani a matsayin halattacciyar Yar takarar APC
“Tare da goyon bayan ku, ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da duk sauran ‘yan takara za su lashe zaben 2023,” inji shi.
Gwamnan ya kuma yi kira ga masu zabe da su yi imani da jam’iyyar su fito gaba daya domin kada kuri’unsu.
Ya bayyana fatansa na cewa zaben 2023 zai kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da magudi ba.
Gwamna Ganduje ya ce maido da masarautar Gaya ya kawo ci gaba da a yankin ta fuskar zaman lafiya da tsaro.
A jawabin da ya gabatar a wurin kaddamarwar, dan takarar gwamna, Nasiru Gawuna, wanda shi ne mataimakin gwamna a yanzu, ya bukaci jama’a. su zabe shi da abokin takararsa, Murtala Garo, domin ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukan alheri na shugaban su Ganduje.
.
Ya yi alkawarin cika alkawuran da ya daukar wa al’ummar jihar idan har aka zabe shi, ya kuma yi addu’ar Allah ya taimake shi ya ci gaba da gudanar da aikin da aka dora masa.
Shima a nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya ce jam’iyyar za ta lashe dukkan mukamai na zabe a zaben 2023 a jihar duba da irin rawar da ta taka a tsawon shekaru.
NAN
