News
Kotu ta tabbatar da aishatu binani a matsayin halattacciyar Yar takarar APC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halattacciyar ’yar takarar gwamnan Jihar Adamawa ta Jami’iyyar APC
Gbajabiamila yayi tir da masu sukar bada bashin kudi ga dalibai.
Aminiya ta rawaito cewa Kotun da ke zamanta a Yola ta jingine hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaben dan takarar gwamnan Jam’iyyar APC da Binani ta lashe.
Ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya sunan Sanata Binani a jerin ’yan takarar gwamnan Jihar Adamawa a zaben 2023.
Advertisements
