Connect with us

News

Buhari Ya Amince Da Siyo Jiragen Yaki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Najeriya na sa ran karbar sabbin kayayyakin yaki na jiragen sama 54, da suka hada da jiragen sama na kai hari da jirage masu saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka.

 

 

Advertisement

Najeriya ta dauki wannan mataki ne don bunkasa karfinta na yaki da tabarbarewar tsaro a kasar, kamar yadda babban hafsan sojin sama Isiaka Oladayo Amao ya bayyana a ranar Alhamis..

 

Rikicin mayaka Boko haram da kuma sace-sacen mutane don neman kudin fansa da wasu ‘yan bindiga a arewa maso yamma, su ne manyan barazanar tsaro ga Najeriya da shugaban kasar na gaba zai fuskanta bayan zaben shugaban kasa da za’a yi a watan Fabarairu mai zuwa.

 

Voice of America ta rawaito cewa Amoa ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da aikewa da sojojin saman Najeriya jiragen yaki samfurin m-346, jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK, jirage masu saukar unugulu na Agusta 109 Trekker da kuma jirage marasa matuki na Wing Loog II da China ta kera, wadannan na daga cikin kayayyakin yakin sama.

 

Advertisement

Sai dai bai bayyana ainihin lokacin da za’a kawo wadannan kayayyaki ba, kuma nawa aka biya na kayan ko wacce kasa ko kuma kasashen da aka sayo su.

 

A bara, Najeriya ta karbi jiragen sama 12 na Super Tucano, shekaru 4 bayan da Amurka ta amince ta sayar ga kasar da ke Yammacin Afirka da jirage masu saukin kai hari domin yaki da masu tayar da kayar baya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending