Connect with us

News

MDD ta nuna damuwa game da batun take ‘yancin bil adama a China

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kwamishinan hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana damuwa game da halin da ƴancin bil adama yake ciki a China inda ya ce a shirye yake ya tattauna da gwamnatin ƙasar game da haka.

 

Advertisement

Volker Turk ya yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya su ci gaba da mutunta ƙa’idojin yarjejeniyar ƴancin ɗan adam ta duniya sai dai China tuni ta yi gargaɗin za ta fice daga yarjeneniyar bayan wani rahoton Majalisar ɗinkin Duniyar ya bayyana yadda take tafiyar da al’amuran da suka shafi musulmin Uighur na iya zama laifi ga bil adama.

Tarayyar Turai ta sanya takunkumi kan mutanen da ke da hannu a rikicin gabashin Kongo

Turk ya ce rahoton da aka gabatar ranar 31 ga watan Agusta, yana da matuƙar muhimmanci. Ya bayyana abubuwan damuwa game da ƴancin bil adama kuma abin da zan mayar da hankali a kai shi ne bibiyar shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton.

Advertisement

 

Mista Turk wanda aka naɗa shi kan wannan muƙamin a watan Oktoba, ya yi waɗan nan kalaman ne domin tunawa da ranar ƴancin ɗan adama

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending