Labarai
Matakin CBN na rage yawan hada-hada da kuɗi zai rage barazanar tsaro, in ji matasan Arewa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Takaita amfani da takardun kuɗi da Babban Bankin Najeriya wato CBN ke kokarin aiwatarwa zai rage barazanar tsaro a Najeriya, in ji ƙungiyar tuntuɓa ta matasan Arewa.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Shettima Yerima ya shaida hakan ne a wani taro da suka yi a Abuja, lokacin da yake tsokaci kan matakin bankin na sake wa kuɗin ƙasar fasali da kuma takaita mu’amala da takardar kuɗi.
Yadda ‘yan bindiga suka yi sanadin rayukan mutum 4 a jihar Imo
Yarima ya ce lura da halin da ake ciki a Najeriya akwai bukatar bijiro da matakan da za su bankaɗo masu rashawa da kuma masu niyyar sayen kuri’un mutane a zaɓen da ke tafe.
Sannan a cewarsa yana ganin wannan mataki zai kuma kawo ko rage matsalolin tsaro a faɗin Najeriya.
Batutuwa biyu wato sauya kuɗin kasa da kuma taƙaita kuɗin da za a karɓa daga banki a rana guda ta ATM ko Pos ya ja hankali sosai a Najeriya.
Yayinda wasu ‘yan kasar ke maraba da matakin, galibi sun yi suka inda suke ganin matakin zai fi tasiri kan talaka da ‘yan kasuwa.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
