News
Yadda ‘yan bindiga suka yi sanadin rayukan mutum 4 a jihar Imo
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya ta ce akalla mutum 4 suka rasa rayukansu, a wani artabu lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ofishin hukumar zabe ta kasa a garin Owerri.
‘Yan sandar sun nuna gawawaki da wasu kayayaki da ‘yan bindigar suka bari bayan musayar wutar.
Man City za ta fadada Etihad da zai ci ‘yan kallo sama da 60,000
A cewar Michael Abattam, mai magana da yawun hukumar ‘yan sandar a jihar ta Imo ya ce an kai wannan hari ne da misalin karfe 3 na safiyar litinni,bayan da wasu ‘yan bindiga guda goma suka tunkaro cibiyar hukumar zabe ta kasa a garin Owerri babban birnin jihar ta Imo.
A cikin artabu da kwashi ba dadi da suka wakana tsakanin ‘yan sandar da ‘yan bindigar, dan sanda daya ya rasu ayayin da mutum uku suka rasa rayukansu daga bangaren ‘yan bindigar, akwai kuma mutum guda da ya samu rauni.
A cewar kakakin ‘yan sandar, maharan sun kai harin ne ta hanyar jefa bama-bamai da aka sarafa da fetur a kan rufin hukumar zaben a lokacin da suka zo cikin wasu motoci guda hudu makare da makamai.
Irin wadannan hare-hare a kan ofisoshin zaɓe na Najeriya ya yawaita a kudancin kasar a wannan lokaci da ake shirye -shiryen gudanar da babban zaben 2023.
