News
Wani babban jami’in Rasha ya tsallake rijiya da baya a Kherson
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Babban jami’i na biyu mafi girma da Rasha ta nada a yankin Kherson na Ukraine ya tsallake rijiya da baya, bayan yunkurin halaka shi.
Jami’ai sun ce an tarwatsa morar Vitaly Bulyuk a garin Skadovsk da ke tsakanin Kherson da Crimea.
Yadda ‘yan bindiga suka yi sanadin rayukan mutum 4 a jihar Imo
A cewar jami’ai, an kashe direbansa, amma Mista Bulyuk yana kwance a asibiti a Crimea cikin wani mummunan yanayi, ko da yake sun ce lamarin da sauki.
An tilastawa sojojin Rasha janyewa daga birnin Kherson a watan da ya gabata, amma sun ci gaba da rike ikon galibin yankunan kudancin kasar.
Advertisements
