Connect with us

Entertainment

Jaruman Kannywood Da Suka yi Aure A shekara 2022

Published

on

Masana,antar kannywoo

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Shekarar 2022 ta bayyana an yi bukukuwan aure da dama a masana’antar Kannywood yayin da fitattun jarumai Maza da mata na masana,antar Kennywood ke auren junan,su

Advertisement

A cikin shekarar, mata guda takwas, ne sukayi aure Kuma uku daga cikinsu sun faru ne a watan Fabrairu kamar yadda daily trust ta rawaito

 

Advertisement

’Yan Bindiga Sun Sace Gomman Fasinjojin Jirgin Kasa A Edo

Daya daga cikin daurin auren na bana ya hada da na Mai Shadda & Hassana da Lilin Baba & Ummi Rahab.

 

Advertisement

Shahararren dan wasan barkwanci kuma kwararre a harkar fastocin fina-finai, Ali Muhammad Idris (Ali Artwork) yayi aure shi da masoyiysrsa Mai suna hauwa,u Muhammad bello Kuma anyi auren a ranar 25 ga Fabrairu, 2022.

An daura auren ne a Masallacin Juma’a na Filin Kashu da ke Unguwa Uku, Kano, kan sadaki Naira 100,000.

Advertisement

Jarumin wanda ake yi wa lakabi da ‘Madagwal’ ya shaida wa mujallar Fim cewa, Naziru M. Ahmad da Isah Bawa Doro ne kawai jaruman Kannywood suka halarci daurin auren.

 

Advertisement

 

A ranar ne Aisha Aliyu Tsamiya itama aka daura auren,ta da masoyin mijinta da misalin karfe 11 na safe a masallacin Sheikh Muhammed Aminu Ibrahim Daurawa dake unguwar Naibawa a jihar Kano.

Advertisement

A lokacin da take shirin aurenta, jarumar ta so komai ya kasance a sirrance amma ta samu labarin a kafafen yada labarai. Da gangan ta fitar da sanarwar cewa ba za a yi bikin auren kamar yadda aka tsara ba.

Aisha ta za6i ta yi wani guntun taron. Wannan shi ne dalilin da ya sa ta bar mutane da yawa mamaki.

Advertisement

 

 

Advertisement

Washegari 26 ga Fabrairu 2022 Hafsat Idris ta yi aure a asirce wanda da farko ta ki tabbatar da aurenta, amma daga baya ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta tabbatar da cewa ta yi aure.

Hafsat Idris, wacce aka fi sani da ‘Hafsat Barauniya’ ta yi aure a asirce da wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa ta auri daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Janar Abacha.

Advertisement

Sai dai a sakon da ta fitar domin nuna jin dadin ta ga mutanen da suka yi mata fatan alheri, jarumar ta ce, “Ina mika sakon godiya ga dukkan abokaina da ‘yan uwa da abokan arziki bisa fatan alheri da suka yi min.

“Amma ina so in yi magana game da jita-jitar da ake ta yadawa cewa mijin da na aura yana da alaka da dangin Abacha, to, wannan ba gaskiya ba ne.”

Advertisement

 

 

Advertisement

Lamarin da ya faro a matsayin fim kawai tsakanin fitaccen furodusan Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda da wata jarumar masana’antar fim, Hassana Mohammed, ta yi aure.

Ma’auratan sun yi aure ranar 13 ga Maris, 2022 a masallacin Juma’a na Murtala da ke Kano.

Advertisement

Dubban jama’a daga ciki da wajen masana’antar shirya fina-finai ne suka halarci daurin auren Fatiha.

Bayan an gudanar da bikin aure ne, furodusan ya dauki hotonsa a dandalinshi na sada zumunta ya rubuta cewa, “Allah sarki! To Allah Subhanahu Wa Ta’ala!! Yayi nufin Aure na da Hassana Mohammad, ina neman addu’ar masoyana don samun nasarar aurenmu.”

Advertisement

 

 

Advertisement

Lilin Baba da Ummi Rahab wasu jaruman Kannywood ne da suka auri juna ranar 13 ga watan Yuni 2022.

Su biyun sun sha bayyana soyayyar juna a Instagram, inda a lokuta daban-daban Ummi ke kiransa da ‘Mijina’ wato mijina.

Advertisement

A ranar haihuwarta a watan Fabrairun 2022, jarumar ta rubuta a Instagram, “Na kusa in yi wuff da ke,” ma’ana nan ba da jimawa ba zan aure

Jaruman Kannywood da suka halarci daurin auren sun hada da Ali Nuhu, Umar M Sherif, TY Shaba da dai sauransu.

Advertisement

 

 

Advertisement

Daya daga cikin jaruman shirin ‘Dadidin Kowa’ na tashar Arewa24, Raliya, wacce ainihin sunanta Amina Lawan ta kuma yi bankwana da masana’antar fim yayin da ta yi aure a ranar 23 ga Yuli, 2022.

Jarumar ta auri mijinta Habibu Abdullahi a tsohon masallacin Juma’a na BUK dake Kano.

Advertisement

 

 

Advertisement

Shahararriyar jarumar Kannywood kuma mai shirya fina-finai, Rukayya Umar Santa (Rukayya Dawayya) ita Kuma an daura aurenta da Babban Daraktan Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Sama’ila Na’abba Afakallah.

Daurin auren da ya gudana a masallacin Juma’a na Tinshama ya kawo karshen rade-radin da ake ta yadawa cewa ma’auratan suna soyayya a asirce.

Advertisement

Dawayya, mahaifiyar daya, ta taba yin aure kuma ta daina yin wasan kwaikwayo bayan auren. An bayyana cewa bayan ta haihu ne auren ya yi karo da ita, inda ta sake yin fim a masana’antar shirya fina-finai.

Da take jawabi bayan daurin auren, Dawayya ta ce ta ji gamsuwa kuma ta yi addu’a ga sauran matan da su samu mazajen aure irin nata.

Advertisement

Jaruman Kannywood da suka halarci bikin sun hada da Adamu Sani, Auwalu Isma’il Marshal, Sani Sule Katsina, Baba Ƙarami, Ado Ahmad Gidan Dabino, Alhassan Kwalle, Alhaji Musa Maikaset, Nura Hussaini, Salisu Officer da dai sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending