News Ku daina karbar tsohuwar Naira – CBN Published 4 years ago on January 19, 2023 By KABIRU BASIRU FULATAN Facebook Twitter Pinterest LinkedIn WhatsApp Copy Link DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN Babban Bankin Najeriya CBN ya umurci jama’ar kasar da su daina karbar tsoffin kudaden da bankunan kasuwanci ke ba su, saboda ganin lokacin daina amfani da su na kara karatowa. Mataimakiyar Daraktan Sarrafa kudaden Bankin, Dr. Rekiyat Yusuf ta bayyana haka lokacin da take fadakar da ‘yan kasuwa a birnin Lokoja dangane da sabunta takardun kudin da bankin ya yi. PSG ta doke Al Nassr 5-4 a wasan sada zumunta. Yusuf ta ce, bankin nasu ya tanadi hukunci mai tsauri akan bankunan kasuwancin da aka samu suna ci gaba da bai wa jama’a tsoffin takardun kudaden wadanda za su daina aiki daga ranar 31 ga watan nan. Daraktar ta bukaci jama’a da su gabatar da korafi akan duk wani bankin kasuwancin da ya ci gaba da bai wa mutane tsoffin takardun kudaden ta kafar na’urar ATM, yayin da ta bukace su da gaggauta kai tsoffin kudaden bankin domin sauya musu su. Jami’ar ta ce babu dalilin da bankunan za su ci gaba da bai wa jama’a tsoffin takardun kudaden domin babban bankin ya yi tanadi na musamman wajen wadata su da sabbin kudaden da aka buga.Advertisement Yusuf ta yi bayani akan dalilan da suka sanya bankin sabunta kudaden da suka hada da dakile ayyukan ta’addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane da cin hanci a tsakanin al’umma da kuma magance hauhawan farashin kayan masarufi. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn WhatsApp Copy LinkAdvertisements Related Topics:Cbnkudi Up Next Ronaldo ya sha naushi a fuska a wasansu da PSG Don't Miss CBN zai hukunta wasu bankuna a Kano kan sabbin kuɗaɗe Advertisement You may like CBN Ya Soke Lasisin Bankunan Microfinance 46 CBN Ya Musanta Samar Da Sabbin Takardun Kudin N5,000 Da N10,000 Kano Da Katsina, Sun Zama Sahun Gaba Wajen Matsalar Rashin Isassun Takardun Kudi Click to comment Leave a Reply Cancel replyYour email address will not be published. Required fields are marked *Comment * Name * Email * Website Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment. Latest Popular Videos News2 days ago Ya Kamata Kowane Dan Najeriya Ya Samu Horon Aikin Soja —Ministan tsaro News2 days ago Akwai Yiwuwar Fuskantar Ɓullar Cutar Ebola Kowanne Lokaci Daga Yanzu — Gwamnatin Tarayya News2 days ago NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero News2 days ago Akalla Mutane 259 Ne Suka Mutu Sakamakon Zazzabin Lassa A Najeriya News3 days ago TINUBU DA SHETTIMA BA SA NAJERIYA — “Ba Ni Ne Mukaddashin Shugaban Ƙasa Ba” — Akpabio News3 weeks ago Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano News3 weeks ago NUJ Kano Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa ’Yan Jarida News4 weeks ago Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna News3 weeks ago Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso News4 weeks ago Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano Trending News6 days ago Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba News4 days ago An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja News5 days ago Mutum 332 Sun Kamu Da Cutar Mashaƙo A Gombe