Kafafen yada labaran kasar Habasha sun yi gargadin cewa, sama da mutane miliyan takwas suna fuskantar barazanar matsanancin kamfar ruwa, a wasu bangarori na arewa maso gabashin Jahar Amhara, waɗanda ke fuskantar mummunan tasirin yakin Tigray mai makwabtaka.
Jami’an shiyyar sun ce, kimanin tashoshin samar da ruwan sha 1500 ne aka lalata a yakin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da mayakan ‘yan tawayen Tigrayan.
An kawo karshen tashin hankalin ne a watan Nuwamba, sai dai yakin ya bar baya da kura, sakamakon karancin abinci da ruwan sha, da cibiyoyin kiwon lafiya, da ake fama dashi a dukkan bangarorin na Tigray da Amhara.
Karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar, mayakan Tigrayan sun amince su aje makamansu, amma har yanzu akwai mayakan dake tittidowa daga kasar Eritrea mai makwabtaka, dake kara mamaye shiyyar.
