News
Lauyoyi a Masar za su tsunduma yajin aiki
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Lawyoyi a kasar Masar sun bukaci mambonsu su shiga yajin aiki na sai baba ta gani.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yankewa wasu lauyoyi ne na zaman gida yari na shekaru biyu, bisa zarginsu da cin zarafin wasu ma’aikatan kotu.
Kungiyar lauyoyi ta kaar Masar ta bayyana matakin da cewa, shine mataki na farko da kungiyar tasu ta dauka a sakakon hukuncin da aka zartarwa lauyoyin shida a binin Mersa Matruh.
Sai dai sun ce zasu daukaka kara.
Advertisements
